Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa Ahlul Bayt (as) - ABNA – ya naklato maku cewa: an yi huduba ne bayan yakin Jamal da kashe Talha da Zubair a shekara ta 36 bayan hijira. Duk da cewa Sayyid Razi kamar yadda ya saba bai bayar da labarin isnadin wannan ruwayar ba, amma an ruwaito isnadin wannan ruwayar a cikin "Bihar al-Anwar" da sharhin Nahjul-Balagha na Allama Majlisi da Minhajul-Baraa' da sharhin Nahjul-Balagha na Qutb Rawandi (R.A). daga Imam Askari (a.s.) daga iyayansa daga Imam Ali As.
Har ila yau Sayyid Razi yana cewa a farkon wannan hudubar da yake siffanta ta: "Tana daga cikin mafificin fasahar maganganunsa (SAW), kuma a cikinta yana kwadaitar da mutane da kuma shiryar da su daga kaucewa bacewa". Wannan hudubar tana da jimloli kusan 10, kuma daya daga cikin siffofinta shi ne cewa kowace jumla ita kadai tana da ma'ana mai amfani akan kanta kuma ana iya raba ta da sauran jumlolin, yayin da aka hadata gaba daya kuma tana da tsari da gini mai kyau.
A mahangar gaba daya abin da wannan huduba ta kunsa yana iya kasuwa kashi uku: shiryar da mutane da ke cikin duhu ta hanyar Ahlul Baiti (AS) don kai su ga kololuwar ci gaba da samuwar farin ciki, tare da mai da hankali kan masu tayar da fitina ta fuskar addini wanda masu fitinar Jamal suka aukar, da goyon bayan mutanen Basra da masu tayar da zaune tsaye, domin hana su da katange su daga fadawa cikin fitinar jama'a a fili, da kuma hana masu tayar da fitina anan gaba.
Wannan hudubar wani sabunta gargadi ne ga al'ummar Basra, don gudun kada su sake adawa da shugaban Musulunci, su ci daba da dagewa akan bata da kura-kurai, musamman da yake a yanzu gaskiya ta bayyana a fili a gare su, kuma dole ne su kasance suna da kunnuwa masu lura da zuciya shiryayyiya domin su fahimce ta.
A Kan Tafarki Biyu Na Shiriya Ko Bata!
Bangare na karshe na wannan huduba ita ce jumlar karshe ta hudubar da Imam ya yi da mutanen Basra. Jumla da za a iya fadinta ga duk wanda ya tsaya kan gaskiya a tsawon tarihi: "A yau, mu da ku mun tsaya kan tafarkin shiriya da bata". Ko kuma, da wata ma’ana, muna cikin tsaka-tsaki tsakanin gaskiya da bata, a yau mu da kumun tsayu akan tafarki kona shirya ko na bata, ku kuma a wata ma’ana! Mun tsayu akan tafarki guda shiriya da bata wanda zamu bi wani tafarki kuma ku bi wani Wannan matsaya ta bayyana a fili ta hanyar nazarin tushen kalmar (tawaqafna) ma’ana tsayawa da kuma bambancinta da “tawafakna” wacce ta ke da ma’ana yarda da sulhu.
A cikin jimla ta ƙarshe, tana cewa: “Wanda ya yi imani da samun ruwa ba zai ji ƙishirwa ba”. Yana nufin cewa mutumin da yake da amintaccen shugaba kuma mai shiryarwa ba zai shiga shakku ba, da jarabawowin shaidan, da damuwa, da rashin amana. Domin yana jin kansa a kusa da maɓuɓɓugar ilimi bayyananne. Amincewa da ma'anar "imamanci" a cikin "aminci da shiriya" na al'umma yana daga cikin muhimman abubuwan da 'yan Shi'a suke da shi.
Madogara:
Littafi: Sakon Imam, Bayanin Nahjul Balaga na Ayatullahi Makarem Shirazi.
Littafi: Masu Riwayar Nahjul-Balagha, Marigayi Muhammad Dashti
Littafi: Bayyanar Tarihi, Bayanin Nahjul-Balagha, Ibn Abi al-Hadid, Mu'utazila.
Littafi: Sharhin Nahjul-Balagha na Ibn Maytham Bahrani, Muhammad Moghadam ya fassara.
Sayyid Ali Asghar Hosseini/ABNA
Your Comment